Kwayar cutar kwanputa ta ‘kashe’ shugaban Facebook

Mark

Wata cutar da ake yadawa a kwamputa, wacce ta samu shafin Facebook, ta sa shafin ya sanar da mutuwar mutane da dama, ciki har da mai Mark Zuckerberg, mai kamfanin na Facebook.

Cutar dai ta sa shafin na sada zumunta ya wallafa wasu bayanai a shafukan Facebook na wasu mutane, wadanda za su nuna wa duk mutumin da ya ziyarci shafukan cewa mutanen fa sun mutu.

Hakan ya sa mutanen sun rika wallafa sakonnin da ke nuna cewa ba su mutu ba domin kawar da tashin hankalin da abokansu ka iya fada wa a ciki.

Kakakin kamfanin na Facebook ya bayar da hakuri a kan wannan gagarumin kuskure suka yi.

Ya kara da cewa,”Wannan ba karamin kuskure ba ne, amma dai mun gyara shi. Muna matukar bayar da hakuri a kan hakan.”

A cewarsa, ana wallafa irin wadannan bayanai ne kawai a shafukan mutanen da suka mutu ta yadda abokansu da ke da rai za su rika tunawa da su, amma sai ga shi an ce mai kamfanin na Facebook na cikin wadanda suka rasu.

Sakon da aka wallafa a shafin Mr Zuckerberg ya ce “Muna fatan mutanen da ke kaunar Mark za su kwantar da hankalinsu sannan su rika tunawa da abubuwan na bajinta da ya yi a lokacin da yake raye.”

Advertisements

Trump zai ci gaba da shirin inshorar lafiya na Obama

Donald Trump

Zababben shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa zai ci gaba da tafiyar da shirin Shugaba Obama na inshorar lafiya.

Soke shirin inshorar lafiyar da ake yi wa lakabi da Obamacare na gaba-gaba cikin jerin abubuwan da Donald Trump ya yi ta nanata cewa zai yi a lokacin yakin neman zabe, yana mai cewa shirin tamkar wani babban bala’i ne ga kasar.

Su ma wasu shugabannin jam’iyyar Republican sun bayyana a babban taron jam’iyyar cewa tsarin inshorar lafiyar tamkar katsalandan ne da gwamnati ke yi a harkar kiwon lafiya.

Sai dai yanzu a wata hira da ya yi da mujallar Wall Street Journal, zababben shugaban kasar ya nuna cewa zai iya ci gaba da aiwatar da wasu muhimman abubuwa da ke kunshe a shirin inshorar lafiyar wadanda ya ce yana matukar so.

Tun bayan nasararwar da aka yi ta yin nasararsa a zaben da aka yi ranar Talatar da ta wuce, Mista Trump yake ta sanar da sauye-sauye kan alkawuran da ya yi a lokacin yakin neman zabensa.

Ya zuwa yanzu dai ya sauya fasalin mambobin kwamitinsa na karbar mulki inda ya ragewa gwamnan New Jersey Chris Christie mukami, sannan ya nada zababben mataimakin shugaban kasa Mike Pence a matsayin mai sanya ido a kan nada jami’ai 4,000 kafin rantsar da shi a ranar 20 ga watan Janairu.

Akwai kuma wasu mukamai da aka ware ga manyan ‘ya’yan Mr Trump din su uku da kuma wasu da ke tsayawa kusa da shi a lokutan yakin neman zabe da suka hada da tsohon magajin garin New York Rudy Giuliani da tsohon kakakin Majalisar wakilai Newt Gingrich.